IYALAN MA'ADINAN 37 DA SUKA MUTU A HANUN NSCDC A NEJA SUN KI AMINCEWA DA N100,000 NA GWAMNATIN JIHA, SUNCE MUNA SON ADALCI
Iyalan wasu daga cikin ma'adinan 37 da suka rasu a hannun jami'an Nigeria Security and Civil Defence Corps (NSCDC) a Jihar Neja sun ki amincewa da tallafin Naira 100,000 da gwamnatin jihar ta ba su.
Iyalan sun ce wannan kudin "kudin jini" ne, kuma gwamnati na kokarin rufe bakinsu ne maimakon ta nemo masu laifi ta hukunta su.
Lamarin ya faru ne bayan NSCDC ta kama mutanen a wani samame da ta yi kan masu hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba a yankin M.I Wushishi da Lukoto a ranar 15 da 16 ga watan Satumba.
Da farko NSCDC ta ce cuta ce ta kashe su, amma daga baya iyalan mamatan da wadanda suka tsira sun ce cunkoso ne da rashin iska a gidan yari ne ya kashe su. An ce mutum 66 aka tsare a daki daya, har wasu suka sha fitsarinsu saboda kishin ruwa.
Wani dan uwa na daya daga cikin mamatan ya ce a video:
> "Eh, suna bamu kudi ne don su rufe mana baki... Sun bamu kudi don su rufe mana baki. Ba za mu ci moriyar jinin yan uwanmu ba."
Wata uwa mai ciki har ta kuka ta ce gwamnati na sanya farashi a kan rayukan 'ya'yansu ne.
GWAMNATI TA DAKATAR DA JAMI'AI 24
Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike. Ministan Harkokin Cikin Gida ya dakatar da Kwamandan NSCDC na Jihar Neja, Suberu Siyaka Aniviye, da wasu jami'ai 24.
Gwamnan Neja, Mohammed Umaru Bago ya ayyana dokar hana fita na awa 12 a Minna saboda zanga-zangar da matasa suka yi.
Amma iyalan mamatan sun ce:
> "Ba kudi muke so ba, adalci muke so. Wanda ya kashe mana yara a hukunta shi."
Yanzu haka ana jiran sakamakon binciken gawarwakin a asibiti don gano ainihin abinda ya kashe su.
Source: Sahara Reporters

0 Comments