Header Ads Widget

Farashin Man Fetur Yafi Sauki Fiye Da Amurka- Ministan mai

 ƘASAR NAJERIYA TAFI KO WACCE ƘASA SAUƘIN MAN FETUR!!!


Ministan Albarkatun Man Fetur, Heineken Lokpobiri, ya bayyana cewa farashin fetur a Najeriya har yanzu bai kai na wasu ƙasashe ba, ciki har da Amurka da wasu manyan ƙasashen Afirka.


A cewar ministan, litar fetur a Najeriya tana kan matsakaicin farashin kusan Naira 1,430, yayin da makamanciyar litar a Amurka ta kai kusan Naira 1,633 idan aka canza kuɗin zuwa Naira. Ya ce farashin ya kai kusan Naira 1,959 a Kamaru, sannan Naira 2,070 a Ghana da Afirka ta Kudu.


Lokpobiri ya yi wannan bayani ne yayin da yake kare matakan da gwamnatin tarayya ta ɗauka na cire tallafin fetur da Shugaba Bola Ahmad Tinubu yayi, da kuma ba da damar kasuwar man ta tafiya bisa tsarin masu zaman kansu.


Sai dai bayanin na zuwa ne a daidai lokacin da ake sayar da fetur kan kusan Naira 1,500 ko fiye a wasu sassan Najeriya, abin da ke ci gaba da haifar da muhawara kan yadda farashin man ke shafar rayuwar al’umma.


A ƊAYAN BANGAREN KUMA, ƊAN TAKARAR SHUGABAN ƘASAR ATIKU ABUBAKAR Gcfr. 

Ya Daga Akan Sai Ya Cire Tallafin Man Fetur, Domin Samun Sauƙin Tsananin Rayuwar Da Talakawan Ƙasar ke ciki.


Tuna Bayan Da Shugaba Tinubu Ya Cire Tallafin Man Fetur A Shekarar 2023, Talakawan Ƙasar Suke Ɗanɗana Kuɗarsu, Sakamakon Hauhawar Farashi, Da kuma Ƙarin Kuɗin


Sufuri
, kuma Yayin da cire Tallafin baya Amfanar Dasu Talakawan.

Post a Comment

0 Comments