DALILAN DA YASA TINUBU YAFI TSORON ELRUFAI AKAN JONTHAN!!!
LABARI
Mutane da yawa suna tunanin abin da zai faru a 2027 zai kasance kamar na 2015, amma a'a. Wannan karon lamarin zai iya zama mafi girma fiye da na 2015.
Shi ya sa ake tsare da Malam Nasir El-Rufai tun watan February.
Banbancin Jonathan Da Tinubu
Jonathan ya kasance shugaba mai bin tsarin dimokuradiyya. Kana iya sukar sa, kana iya ma yi masa suka mai karfi a Facebook, amma ka koma gida ka kwanta lafiya. Wannan ba tsoro bane, shugabanci ne.
Tinubu ya shafe shekaru yana sukar Jonathan, amma Jonathan bai taba tura DSS, EFCC ko ICPC su je su kama shi ba. Ya bar kafafen yada labarai su yi aikinsu, ya bar kotuna su gudanar da aikinsu.
Ko lokacin da Obasanjo ya rubuta masa doguwar wasika mai shafuka 18 yana sukar sa, Jonathan ya amsa cikin ladabi. Kuma lokacin da ya sha kaye a zabe, ya amince da sakamakon ya sauka akan mulki.
Amma lamaran Tinubu ya bambanta. A karkashin gwamnatinsa, yunwa da fushin jama'a sun karu, ana zargin ana tsangwamar masu adawa, yayin da damar da mutane ke da shi na bayyana ra’ayinsu yake kara yin kasa.
HaÉ—in Guitar 2015 Da Sabon Salo Na 2027
A shekarar 2015, Malam yana daga cikin mutanen da suka taka muhimmiyar rawa wajen gina hadin gwiwar da ya kai ga kafa APC. Yayin da wasu ’yan siyasa suka fi mayar da hankali kan taruka da gangami, El-Rufai ya mayar da hankali kan tsara yadda za a hada kungiyoyi da jam’iyyun siyasa.
CPC, ACN da ANPP suka hadu suka kafa APC. Wannan hadin gwiwar ya taimaka wajen samar da hanyar da ta kai Muhammadu Buhari ga nasarar zaben 2015.
Amma tsarin Malam na 2027 yana bukatar abubuwa uku: Tafiya mai karfi da ba za a iya saka ta ba a aljihu ba, Gungun jama'a da zasu yada wannan tafiya, da kuma hadin kan shugabannin siyasa tare da jama'ar da matsalolin rayuwa ta shafa.
A 2015 mutane suna neman CANJI. Amma a yau, mutane suna neman TSIRA ne. Mutumin da yake neman canji zai iya jira, amma mutumin da yake neman yadda zai tsira ba zai iya jira ba.
A 2015 abin da ya faru shi ne hadin kan jam’iyyun siyasa. Amma a 2027, idan aka samu hadin kai, zai iya zama hadin kan jam’iyyu da kuma hadin kan al'umma gaba daya.
Yan kasuwa mata, dalibai, matasan da suka kammala karatu ba tare da aikin yi ba, manoma da ke fama da matsalolin noma duk suna fuskantar matsaloli iri daya. Ba sai an kira taro ba kafin su fahimci cewa suna da matsala guda.
Me Yasa Ake Tsare Malam Nasir?
An so a cire El-Rufai daga harkokin siyasa, a kuma hana shi yin magana. Ana amfani da ICPC ne ta hannun ofishin NSA, maimakon EFCC. EFCC tana karkashin kulawar jama'a sosai saboda yawan bayyanarta a kafafen yada labarai, yayin da ICPC ba ta cika yin hayaniya ba. Ana amfani da wata hukuma da doka wajen cimma wata manufa ta siyasa.
Malam ya san abin da NUHU RIBADU zai iya yi, domin ya taba fuskantar irin wannan yanayi a baya. Saboda haka, ya riga ya shirya ma hakan.
ELRUFA'I DA ADC
Kafin a tsare Malam, ya shiga ADC, ya taimaka wajen gina hadin gwiwar jam’iyyun adawa, sannan ya tattauna da H.E Atiku Abubakar, David Mark da sauran shugabanni. Babu wata jam’iyya guda da za ta iya kawar da Tinubu ita kadai. Sai an hada karfi.
Za a iya tsare mutum, amma ba za a iya tsare ra’ayinsa ko sakonsa ba. Tsare El-Rufai na iya kara sanya mutane su kula da abin da yake fada da kuma abin da hadin gwiwar ADC ke kokarin cimmawa.
Ya shirya kansa tun kafin a tsare shi. Ya san cewa zaman tsarewa na iya daukar lokaci, kuma ya yi magana a kan hakan tun kafin a kama shi.
Malam ya riga ya yi tunanin abin da zai faru kafin a fara wasan. Ya yi imanin cewa nasarar ta riga ta tabbata.

0 Comments