ZA KU BASHI?: Ku Kara Ba Mu Dama Mu Kammala Abinda Muka Fara - Tinubu Ya Roki Yan Najeriya
LABARI
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya nemi ’yan Najeriya su kara ba gwamnatinsa lokaci domin ta kammala sauye-sauyen da ta fara.
Shugaban ya bayyana hakan ne a sakon da Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya isar a madadinsa yayin Sallar Juma’a ta musamman da aka gudanar a Masallacin Kasa da ke Abuja.
A cewar Tinubu, gwamnatinsa na kokarin gyara kura-kurai da damar da gwamnatocin baya suka rasa, yana mai kira ga ’yan Najeriya da kada su yanke kauna.
Shugaban ya ce Najeriya na kan hanyar samun ci gaba, kuma zaman lafiya da bunkasar tattalin arziki za su dawo yayin da ake ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen gwamnati.
Ya kara da cewa ya kamata ’yan Najeriya su kara bai wa gwamnatinsa dama domin ta kammala ayyukan da ta fara.
Ku kara ba mu dama mu kammala abunda da muka fara" - Tinubu
Shin a ganinku ya kamata a kara bashi dama?
Ku bayyana ra'ayinku a sashen sharhi


0 Comments