Header Ads Widget

Zamu Samarwa Matasa Milyan Ɗaya Aiki- Shettima

Gwamnatin Tarayya Zata Samarwa Matasa Miliyan Ɗaya Aiki A Ƙasashen Waje Daga Gida Najerya Har zuwa 2030- Inji Kashim Shettima.




New York / Abuja - 28 ga Satumba, 2026


Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirin samar wa 'yan Najeriya aikin yi miliyan daya a kasashen waje wanda za su rika yi daga gida Najeriya nan da shekarar 2030.


Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da shirin Hire From Nigeria a New York, kamar yadda jaridar Aminiya ta ruwaito.


Shettima ya ce Najeriya na da matasa kwararru a fannin fasaha da suka iya Turanci, wadanda za su iya amfana da wannan damar ta yin aiki daga nesa (remote work).


Yadda Shirin Zai Yi Aiki:


Shirin na Hire from Nigeria wanda kungiyoyin Tech4Dev da Univelcity ke jagoranta tare da tallafin gwamnati, na da nufin hada kwararrun 'yan Najeriya da kamfanoni da masu daukar ma'aikata daga kasashen waje.


Me Hakan Ke Nufi Ga Matasan Najeriya?


Wannan dama ce ga matasa masu ilimin kwamfuta, zane-zane (graphics), rubutu, da koyarwa da za su iya neman aiki a kasashen waje ba tare da sun fita daga Kasar ba


Idan kana da sha'awar irin wannan aikin, ka cigaba da bibiyar shafinmu, za mu kawo muku yadda ake cike wannan aikin.


Majiya: Aminiya / Facebook


 Yadda Matasa A najeriya Za Su Nemi Aikin Miliyan Daya Da Gwamnati Ta Ce Za Ta Samar Daga Gida


Bayan sanarwar Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima kan shirin _Hire From Nigeria_ na samar da ayyukan kasashen waje miliyan daya, ga yadda zaka shirya kanka:


Mataki 1: Koyi Wata Fasaha (Skill)

Ayyukan da kasashen waje suke bayarwa daga gida galibi sune:

- Rubutu da fassara (Content writing)

- Zane a kwamfuta (Graphic Design)

- Shirya bidiyo

- Talla a Facebook / TikTok

- Koyar da Turanci a online

- Programming


Mataki 2: Ka bude bayanan ka (Profile)

Shirin na Hire From Nigeria yana hadin gwiwa da Tech4Dev da Univelcity. Idan sun bude portal, za su bukaci:

- CV naka da Turanci

- Hoton ka

- Bayanin fasahar da ka iya

- Link na ayyukan da ka taba yi (ko da a Facebook ne)


Mataki 3: Ka Kula Da Yan Damfara

Gwamnati ba za ta karbi kudi ba don ba ka aiki. Duk wanda ya ce ka biya N5,000 don a saka ka a Hire From Nigeria, damfara ne. Ka guje shi.


Shawara Ta Musamman Ga Masu Karatu A Kishi:

Idan kana da waya da data, ka fara da kanana a shafukan kamar Upwork, Fiverr, ko LinkedIn kafin shirin gwamnati ya kammala. Yanzu lokaci ne na koyo.


Muna nan  muna iya koya maka yadda ake bude profile mai kyau. Tuntube mu: 0811 747 9303


Za mu kawo muku link din rajista da zarar gwamnati ta bude shi a hukumance.


Majiya: Tech4Dev, Aminiya




Post a Comment

0 Comments